Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk da Kudurin Tsagaita Wuta Fada Ya Barke A Syria Jiya Lahadi


Taron Majalisar Dinkin Duniya akan Syria
Taron Majalisar Dinkin Duniya akan Syria

Wani sabon fada ya barke a Syria jiya Lahadi bayan da Majalisar Dinkin Duni ta amince da kudurin tsagaita wuta domin a yi aikin jinkai har na kwanaki 30

Jiya Lahadi wani sabon fada ya barke a kusa da Damascus, duk da bukatar da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, tayi ta tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki 30, domin bada damar gudanar da ayyukan ceto da kuma bai wa maaikatan jinya damar shiga cikin yankin.

Kungiyar nan mai sa ido kan kare hakkin bil Adama a Syria, dake da babban ofishin ta a Birtaniya, tace an kashe wani yaro guda kana sama da mutane 12 suna fuskantar matsalar nunfashi sakamakon harin Sinadari mai guba na Chlorine da aka kai a gabashin yankin Ghouta wanda ke kusa da Damasscus, wannan abin ko ya faru ne a jiya lahadi.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce shugabannin kungiyoyin mayaka dauke da makami sune suka shirya wannan harin na guba domin shafa wa gwamnatin Syria kashin kaji cewa tana anfani da makami mai guba.

Wannan bayanin na dauke a cikin wata sanarwar dake cewa al’amurra a yankin gabashin na Ghouta sai kara muni suke yi.

Haka kuma mutane 9 sun rasa rayukansu yayin da wasu 31 suka samu rauni a wajen babban birnin kasar ta Syria, wannan ya kawo adadin Karin yawan mutanen da suka mutu ya haura 500 a fadan da akayi a cikin satin da ya gabata.

Shugaban Kungiyar sanya idanu kan al'amuran na Syria,Rami Abdel Rahaman, yace a bisa dukkan alamu hare-hare ta sama sun ragu, amma kuma na kasa ya kara Kamari.

Kafofin yada labarai mallakar gwamnati sun ce sojojin gwamnati sun samu damar kara kutsawa cikin gundumar Ghouta dake gabashin babban birnin kasar, sai dai kuma sojojin dake yaki da na gwamnati sun musantawa cewa sojojin gwamnati sun samu wani ci gaba a bakin dagar.

Cibiyar yada labarai ta Ghouta, wadda ta masu yakar gwamnati ce, ta ce dakarun wasu 'yan tawaye da ake kira Rundunar Islama sun tare hanyar sojojin gwamnati, suka kashe wasunsu da dama.

Janar Mohammed Baqeri na kasar Iran, yace kasarsa, wadda ke mara wa shugaba Bashar Al-Assad baya, yace kasarsa tare da Syria zasu mutunta kudurin na MDD.

Sai dai kuma Baqeri ya fada cewa yarjejeniyar tsagaita wutar ba ta hada da unguwannin bayan garin Damascus da yace suna hannun 'yan ta'adda ba.

Shiko dan fafitikar kare hakkin bil adaman nan na Ghouta Ahmad Khanshour yace gwamnatin Assad dama magoya bayan ta basu mutunta kwamitin tsaro na MDD ba domin ko sunyi gaban kansu sun kai mummunan hari a Ghouta daga sassa daban-daban bayan ko an riga an cimma matsaya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG