Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci a Tsagaita Wuta a Siriya


Barin wuta a gabashin Ghouta.
Barin wuta a gabashin Ghouta.

Yayin da ake ta barin wuta babu kakkautawa a Siriya, Manzon Majalisar Duniya Na Musamman Staffan de Mistura ya yi kiran da a gaggauta tsagaita wuta ba tare da bata lokaci ba.

Manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman Staffan de Mistura yau Jumma’a ya yi kiran da a gaggauta tsagaita wuta a Siriya don a kawo karshen abin da ya kira ruwan bama-bamai “mai firgitarwa” da ake yi kan gabashin Ghouta da aka mai kawanya da kuma cilla rokokin da ake yi kan birnin Damascus babu kakkautawa.

A wani bayanin da wata mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya a Geneva ta karanta, de Mistura ya ce dole ne kasashe ukun nan da su ka bullo da ‘tsarin Astana’ – wato da Rasha da Iran da kuma Turkiyya - su gaggauta ganawa da zummar sake shata wuraren da aka haramta fada cikinsu a Siriyar.

Kalaman na de-Mistura sun zo ne ‘yan sa’o’i gabanin wata kuru’ar da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya zai kada kan kudurin tsagaita wuta na tsawon kwanaki 30 a fadin Siriya.

A halin da ake ciki kuma jiragen yaki na gwamnatin Siriya, tare da taimakon Rasha, sun yi luguden wuta kan wuraren ‘yan tawaye da ke gabashin Ghouta har zuwa yau Jumma’a, rana ta shida a jere, su ka hallaka mutane akalla biyar, a cewar ‘yan gwagwarmayar adawa da kuma kungiyar saka ido kan yakin.

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya tsai da karfe 11 na safiyar yau dinnan Jumma’a a Birnin New York, don kada kuru’a kan daftarin kudurin na aiwatar da yarjajjeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki 30 da kuma kawo karshen kawanyar da aka yi ma gabashin Ghouta, don a samu kai kayan agaji da magunguna.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG