Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kira A Tsagaita Bude Wuta A Syria


Majalisar Dinkin Duniya-Syria
Majalisar Dinkin Duniya-Syria

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, (MDD) ya amince bai daya a jiya Asabar cewa, bangarori masu yaki a kasar Syria su fara aiwatar da shirin tsagaita wuta na fadin kasar baki daya, a kalla kwanaki talatin kuma a cire shingaye da aka sa a wasu wurare ciki har da gabashin Ghouta.

Hadin kan da kwamitin sulhun ya samu ya biyo bayan zazzafar tattaunawa na kwanaki a kan bullo da tsarin da Rasha zata amince da shi. An cimma wanna mataki ne bisa kudurin da kasashen Sweden da Kuwait suka aiki a kansa har izuwa kada kuri’ar.

Wakilin Kuwait a MDD Mansour al-Otaibi, yace mu san cewa wannan kudurin ba zai magance matsalolin kai kayan agaji da ake fama da shi a Syria nan da nan ba. Sai dai muna ganin wannan alama ce ta samun nasara. Yace yanzu za a iya aiwatar da kudurin.

Kudurin ya bukaci bangarori masu yaki su tsagaita kisar kiyashi bada bata lokaci ba, na akalla kwanaki talatin a jere kuma su bada daman shiga da kayan taimako ga mabukata kuma a kwashe wadanda suka fama da tsananin ciwo da masu rauni. Sai dai wannan matakin, baya aiki a kan kungiyoyin yan ta’adda kamar IS da Nusra Front ko kuma al-Qaida.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG