Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Ki Amincewa Da Kudurin Tsagaita Wuta A Syria


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Jiya Alhamis kasar Rasha ta bayyana kin yardarta da sabon kudurin Majalisar Dinkin Duniya akan tsagaita wuta har na tsawon kwanaki 30 a yakin Syria lamarin da ake gani wata dabarar baiwa gwamnatin Syria damar gamawa da 'yan tawayen kasar

Jiya Alhamis ne Kasar Rasha ta bayyana kin yardarta da wani sabon daftarin kudirin Majalisar Dinkin Duniya, MDD, dake neman a tsagaita wuta na tsawon kwanaki 30 a fadin kasar Syria, da kuma kawo karshen farmakin da ake kaiwa kan garin Ghouta.

A wani zama na Kwamitin Sulhun MDD da kasar Rasha ta bukaci a yi, jakadanta yayi watsi da wannan neman tsagaita wuta, da kuma bude hanyoyin kai agaji da kwashe marasa lafiya a zaman abinda ba zai yiwu ba.

Wakilin kasar ta Rasha, Vasilly Nebenzia, ya fada wa wakilan Kwamitin Sulhun cewa, "ku saurara kuji, abinda muke bukata ba wai babatu masu dadin ji ba ne, a’a shawara muke so wadda za a iya dauka, wadda kuma zata zo daidai da abinda ke faruwa na zahiri a kasa, don haka Kwamitin Sulhu na bukartar cimma shawara wadda za a iya aiwatar da ita, ba wai ta neman suna ko kuma wadda ba t5a dace da zahiri ba."

Nebenzia ya soki irin labaran da ake yadawa dangane da matakan sojan da gwamnati ke dauka kan tungar 'yan tawaye ta gabashin Ghouta, ya kuma bayyana shi a matsayin wani kanfe da akeyi da niyyar ganin an bata wa kasar Syria da Rasha suna kamar yadda akayi a wani lokaci can baya.

Haka kuma ya soki kungiyar farar hula wadda aka fi sani da suna WHITE HELMET da cewa tana da kyakkyawar dangantaka da ‘yan ta'adda kuma tana aiki kamar wata kafar bada labaran karya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG