Akalla Mutane 14 ne suka makale a cikin wani ramin hakar ma'adinai dake yammacin kasar Ghana bayan da ya rufta.
Hadarin ya auku ne a yankin Prestea dake da tazarar tafiyar kilomita 200 daga Accra, babban birnin kasar.
Rahotannin sun ce mahaka 19 ne suka shiga cikin ramin amma mutum biyar ne kacal suka fito daga ciki bayan da ramin ya rufta.
Ghana dai ita ce kasa ta biyu da ta fi arzikin zinare baya ga Afrika ta Kudu a nahiyar Afirka.
Mafi yawan masu hakar ma'adinan na yi ne ba bisa ka'ida ba duk da dokokin da gwamnati ta sa na hana hakar ma'adinan.
Saurari rahoton da abokin aikinmu Baba Yakubu Makeri dake bibiyan labarin ya hada mana daga Washington D.C.:
Your browser doesn’t support HTML5