Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Mutane 80 A Wani Jirgi Da Ya Nutse


Wani Kwale Kwale dauke da bakin haure ya nutse dauke da mutane inda jirgin yaki Britaniya ya kwashe wadanda aka ceto.

Har yanzu akwai mutane da dama da ba a gansu ba, kuma ana kyautata zaton ruwa ya cinye su a bayan da wani kwale-kwalen roba dauke da mutane fiye da 100 ya nutse a dab da gabar Libya cikin wannan makon.

Hukumar Kula da Kaurar Al’umma ta Duniya ta ce kwale-kwalen ya fara nutsewa ‘yan sa’o’i kadan a bayan da ya bar kasar dake Afirka ta Arewa. Wani jirgin ruwan dake wucewa a lokacin ya ceto mutane 80, ya mika su ga wani jirgin yakin Britaniya mai suna HMS Echo wanda ke cikin tawagar jiragen ruwan yakin Tarayyar Turai masu kokarin dakile safarar mutane a tekun Bahar Rum.

Mai Magana da yawun hukumar ta IOM, Flavio di Giacomo, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa bakin hauren basu san tsawon lokacin da aka shafe kafin a ceto sub a, amma sun rike wasu gabobin wannan jirgi a cikin ruwa har zuwa cikin dare a lokacin da aka cece su.

Hukumar ta ce har yanzu akwai mutane sittin da ba a san inda suke ba.

Jirgin ruwan yakin Britaniya HMS Echo ya gudanar da ayyukan ceto mutane sau da dama cikin wannan makon a teku, inda a jiya jumma’a ya mika mutane 550 ga hukumomi a birnin Brindisis mai tashar jiragen ruwa a kasar Italiya.

Dubban ‘yan Afirka su kan bi ta wannan barauniyar hanya mai tsananin hatsari wajen kokarin kaiwa ga Turai. Kusan dubu 100 sun isa nahiyar ya zuwa yanzu cikin wannan shekara, dubu 10 cikinsu a wannan satin kawai.

Mutane fiye da dubu 2 sun mutu cikin teku a kokarin kaiwa ga Turai a bana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG