Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari a Sansanin 'Yan Gudun Hijira a Nijar


Sojoji suna sintiri
Sojoji suna sintiri

Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashen da ke fama da hare-haren kungiyar Boko Haram, inda ta kan yi fama da hare-hare a lokuta da dama. A baya nan, kungiyar ta Boko Haram ta kai hari a garin Kalambewa.

Da misalin karfe goma na daren jiya ne wasu 'yan kunar bakin wake guda biyu suka tarwatsa kansu a sansanin 'yan gudun hijira dake garin Kabalewa dake cikin jihar Diffa.

'Yan kunar bakin waken dai nan take suka rasu kuma daga 'yan gudun hijiran mace daya da namiji daya sun rasa rayukansu.

Baya ga mutane hudu da suka mutu mutane 11 suka ji rauni.

Gwamnan jihar Diffa ya kama hanyar zuwa garin Kabulewan domin tabbatar wa idanunsa abun da ya wakana a lokacin hada wannan rahoto.

Malam Yahaya Godi magatakardan ofishin jihar Diffa ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Gwamnan jihar Diffan Malam Lawal Dandano shi ma ya tabbatar da aukuwar harin.

A saurari rahoton Haruna Mamane Bako domin jin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG