Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliya A Ghana Tayi Dalilin Mutuwar Mutun Guda.


GHANA: Nasihu Abubakar Ali, dan Ghana malami a New York University
GHANA: Nasihu Abubakar Ali, dan Ghana malami a New York University

An samu ambaliyar ruwa a yankin Kumasi dake gundumar Ashanti na kasar Ghana, hakan ko ya biyo bayan ruwan sama da akayi har na tsawon saoi 3 ba kakkautawa kamar da bakin kwarya.

Wasu daga cikin unguwannin da abin ya shafa ko sun hada da Aboabo,Asebi da kuma Asokore Mampong.

Ita ma tafkin nan da ake kira Pelele ta fuskanci wannan ambaliyar, wannan yasa jamaan dake zaune a wannan yankin anfani da wata gadar da suka yi da hannun su domin tsallaka wannan ruwa.

Sakamakon wannan lamari har anyi hasarar rai guda.

A hirar su da Baba Yakubu Makeri Shugaban wannan gundumar da lamnari ya shafa Alhaji Alidu Seidi ya shaidawa Baban cewa Mataimakin shugaban kasar Ghana Alhaji Mamuda Bamiya ya ziyarci wannan wuri da wannan hadarin na ambaliya ya shafa. Kuma ya gana da sarakunan yankin.

Alhaji Alidu yace sun shaidawa mataimakin shugaban kasan cewa an taba alkawari za a gyara wannan wurin amma ba a gyara ba.

Mataimakin shugaban kasar ya nemi hadin kan shugaban gundumar da Ministan dake kula da yankin suje su duba wurin da za ayi wannanaikin kuma su bashi jimlarkudin da ake bukata domin gudanar da wannan aikin, yace daga yau anyi sati guda zuwa biyu da wannan maganar kuma Alhaji Alidu da Ministyan da kuma Injiniyan sun samar da wannan adadin kudin da aikin ke bukata.

Yace bayan sun gama wannan aiki kuma amma lokacin da zasu kaima mataimakin shiugaban kasa sakamakon wannan bincike nasu shine sai tafiya ta kama shi zuwa China, kuma bai dawo ba sai daf da lokacin bikin Sallah.

Ga Baba Yakubu Makeri da ci gaban wannan tattaunawar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG