Wasu ‘yan bindiga sun budewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Libiya wuta jiya Laraba, sun kuma kama wakilan Majalisar ta Dinkin Duniya su bakwai.
Wani mai magana da yawun MDD ya ce tawagar na tafiya ne tsakanin birnin Tripoli da garin Surman a yammacin Libya yayinda ‘yan bindigar suka fara harbinsu. Sun lalata daya daga cikin motocin tawagar, amma jami’a 7 da suka kama na dan lokaci, sun sake su ba tare da yi musu wani lahani ba.
MDD ta godewa jami’an gwamnatin Libya da hukumomin yankin don kokarin da suka yi na tabbatar da cewa sun kare jami’an. Majalissar ta kuma ce jami’anta dake Libya za su cigaba da goyon bayan zaman lafiya da tsaro a kasar.
Facebook Forum