Baya ga faduwar farashin gangar Mai a kasuwar duniya, da ya sa tsohowar Gwamnatin Najeriya, rage Naira goma a litar Mai wani kalubale na tukarowa na raguwar darajan hannayen jarin kasar China da Japan, da kasashe masu tasowa ke ma’amala kasuwanci dasu.
Wani masanin hanyoyin suba jari, Mansur Manu Sorro, na nuna damuwar faruwar wannan lamarin ta hanyar da tattalin arziki ke samun koma baya ga tarin jama’a.
Yace” idan aka ce an magance damuwa yau ana haiyayyafa mutane kara yawa suke yi haka dai za’a ci gaba da tafiya ana magace damuwa din sannan ana kokarin yadda za’a ga cewa an fuskanci damuwar dake gaba.”
Shin yaya al’uma zasu gane tasirin wannan raguwar darajan hannayen jari daular China, ga kasashe masu tasowa.
Hashimu Muhammad, mai nazari kan tattalin arziki, yace wannan zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki saboda karancin samarwar da Kamfanunuka suke dashi sakamakon wannan koma baya na tattalin arzikin duniya da kasashen ke samun kansu a ciki wanda irin wannan ya shafi Spain, ya shafi Amurka kanta kuma yanzu haka kasar Greece an tallafa an tallafa ama har yanzu tattalin arzikin ta bai farfado ba.
Your browser doesn’t support HTML5