Sakataren yace hakika ko shakka babu kowane lokaci daga yanzu Najeriya zata shiga cikin ayarin kasashen duniya da basu da cutar shan inna.
Babbabn sakataren ya yi furucinsa ne yayin da ya ziyarci wata cibiyar kiwon lafiya ta matakin farko a birnin Abujan Najeriya domin gani ma idonsa yadda hukumomin kiwon lafiya a kasar ke kula da lamuran lafiya da kuma tsaftace muhalli.
Ban Ki-moon yace a matsayinsa na babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya yana aiki kafada da kafada da hukumar kiwon lafiya ta duniya saboda 'yantar da kasashen duniya daga cutar shan inna.
Yanzu dai kasashe biyu suka rage a duniya da suke da cutar ta shan inna. Kasashen kuwa su ne Afghanistan da Pakistan.
Shugaban hukumar kiwon lafiya ta matakin farko Dr. Ado Muhammad na alwashin cewa wannan nasara da aka samu ba zata bari a mayar da hannun agogo baya ba.
Yace kokarinsu shi ne kawar da cutar daga karkara. Saboda haka zasu cigaba da bada rigakarfi har zuwa shekarar 2017 babu rike hannun yaro. Zasu cigaba da bi gida-gida babu sassauci. Yace hukumar kiwon lafiya ta basu tabbacin goyon baya har sai sunsami takardar da ta tabbatar kasar ta kubuta.
Malaman addini irinsu Shaikh Zakariya dake kamfen din yaki da cutar shan inna na farin cikin nasarar da aka samu. Yace ba yahudawa ba ne suka yi maganin kuma shan shi ba yahudanci ba ne. Idan wasu a kasashen musulmi sun sha sun warke me yasa musulman arewa ba zasu sha ba. Hana shan shi ne yahudancin saboda 'yan'yan arewa su cigaba da zama guragu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya