Makon jiya ne shugaban Najeriya ya baiwa hukumomin 'yansanda umurni da suka kara yawansu da mutane dubu goma saboda inganta harkokin tsaro.
Biyo bayan umurnin ne wasu 'yandamfara suka fara fitar da takardun bogi na daukan sabbin 'yansanda alhali kuwa hukumar bata kammala shirin fara daukan ma'aikatan ba.
Dalili ke nan da kwamandan 'yansanda ta biyu dake Kano ya fito yana yiwa jama'a kashedi. DIG Yakubu Muhammad Daudawa na hukumar 'yansandan yace umurnin da aka basu su dauki karin 'yansanda dubu goma yana nan kuma zasu bi.
Kafin su fara daukan sabbin 'yansandan akwai abubuwa da dama da zasu yi inji Yakubu Daydawa.Yace sai sun kasasu kashi uku. Akwai wadanda za'a dauka kurata. Akwai wadanda za'a daukesu a matsayin sifetoci. Akwai kuma masu anini daya wato DSP ke nan.
Yace kawo yanzu basu tallata ba. Basu yanke lokacin da zasu fara ba har yanzu. Yace saboda haka kada kowa ya bari a yaudareshi da cika takardar bogi wadda basu suka bayar ba. Duk wanda ya bayar da kudinsa saboda ya cika wata takarda ya yi hasara.
Hakazalika babban jami'in fayyace daukan 'yansanda ya yi bayanin hanyar da zasu bi wajen sanarda 'yan Najeriya masu sha'awar shiga aikin. Yace zasu buga a jaridu. Za'a fada a gidajen rediyo da hanyar sadarwa. Zasu kuma tura jihohi.
Saboda gujewa 'yandamfara za'a bayyana inda za'a samu fom da kuma inda za'a kaisu. Kada kowa ya ba wani kudi. Su tabbatar an buga a jarida su kuma bi ka'idojin da zasu gindaya.
Ga cikakken bayani.