Shugaba Barack Obama, na ci gaba da maida hankali kan yunkurin da yake yi na rage yawan hayaki da ke gurbata yanayi.
A yau Litinin, Obama ya ke shirin gabatar da wani jawabi a taron koli da ake yi a Las Vegas da ke nan Amurka.
Wannan taro na zuwa ne, yayin da shugaban na Amurka, ya dawo daga hutun makwanni biyu, inda zai fuskanci wasu muhimman batutuwa da ke tunkararsa a ‘yan watannin da ke tafe.
Daga cikin batutuwan, akwai shirin yarjejeniya da aka kulla da Iran game da makamashin nukiliyanta, shirin da ‘yan majalisun dokokin kasar kewa kallon hadarin kaji.
Sai dai yayin da kasashen duniya ke kokarin ganin sun cimma matsaya kan matsalar gurabtar yanayi nan da karshen shekarar nan, shugaba Obama ya himmatu wajen ganin ya gudanar da wasu aikace-aikace na cikin gida, da za su taimaka wajen rage yawan hayakin da ma’aikatu ke fitarwa, da ke illa ga yanayi.