A yau Litinin shugaban Faransa Fraoncois Hollande, ya karrama wasu Amurkwa uku da wani dan Burtaniya da lambar yabo mafi girma a kasar, bayan da suka dakile harin da wani dan bindiga ya yi niyyar kaiwa a jirgin kasa.
A bikin karrama mutanen da aka gudanar a Paris, an ga Mr Hollande ya na lika lambobin yabon a jikin rigunan Chris Norman dan kasar Burtaniya da Spencer Stone da Alek Skarlatos da kuma Anthony Sadler, wadanda Amurkawa ne.
Shugaban na Faransa ya ce irin jarumtakar da mutanen suka nuna, sako ne da ke nuna irin yadda mutane ke shirye su ba da hadin kai wajen yaki da ayyukan ta’addanci.
Mr Hollande ya nanata cewa irin barnar da dan bindigar ya yi niyyar yi, ba za ta misaltu ba, da ba dan wadannan mutane sun sadaukar da rayuwarsu ba.