Wannan shi ne mabanbancin ra'ayi daga wasu 'yan boko ko tsoffin 'yan mjalisa da ya saba da yadda wasu ke korafin yawan kudaden albashin 'yan siyasa da manyan jami'an gwamnati.
Sanata Hadi Sirika ya bayyana nashi ra'ayin akan batun. Yace a matsayinsa na dan majalisa sai da ya dauki kudaden da aka bashi ya hada da na hannusa ya sayawa mutane kaya tare da biyan bukatunsu. Idan da ba'a bashi kudi ba daga majalisa babu yadda zai ya yin abubuwan da ya yi.
Yace tunda ya zama dan majalisa daga 2003 zuwa yau bai taba tashi wata safiya ba bai taimaki mutane goma zuwa ashirin ba. Kullum za'a samu mutane fiye da ashirin a kofar gidansa saboda suna tunanen ana bashi kudi ne ya basu.
Sanata Sirika ya cigaba da cewa akwai wanda zai fadi zabe sai a daukeshi a bashi minista. Yana iya kashe nera biliyan daya yadda ya ga dama. Sai ya dinga bada kwangila yana karbar kashi goma ya sa a aljihunsa. Wani zibin ma ministocin suke baiwa kansu kwangila. Yace minista daya sai ya yi shekara daya amma sai ya kwashi nera biliyan goma zuwa ashirin. Domin ya zauna lafiya sai ya nemo wani dan majalisa da alkali ya jibga masu kudi. Maganar ba ta albashi ba ce. Barnar da ake yi ta fi ta albashi.
Wasu 'yan majalisa suna ganin inda Shugaba Buhari zai bi shawarwari uku ko hudu to da batun samun kudi ko rage albashi ya kwanta. Umaru Barambu dan majalisar wakilai yace inda shugaban zai inganta tsaro, ya yi maganin cin hanci da rashawa da yin maganin zauna gari banza, wato wadanda suka gama karatunsu amma basu da abun yi da zai samu kudin da yake bukata. Akwai kuma abu na hudu ita ce maganar wutar lantarki.
A sashen zartaswa gwamna Al-Makura na jihar Nasarawa yace gyaran zai samu ne idan shugaba Buhari ya hada da mara bayan har wadanda basa karban albashi. Yace idan mutane suka zauna suka yi abun da ya kamata to kasar zata fita daga cikin kangin da ta samu kanta. Zata kafa wani turba da zai ba al'ummar kasar kyakyawan mazauni har abada.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5