A cigaba da gwagwarmayar ganin an kafa Hukumar Farfado Da Yankin Arewa Maso Gabas, “Northeast Development Commission” a Turance; ‘yan Majalisar Dattawan da su ka fito daga yankin sun ce sun kuduri aniyar ganin sun samu hadin kan takwarorin aikinsu wajen ganin an kafa hukumar saboda Boko Haram sun yi mummunar barnar da gyara ta zai yi wuya ba tare da kafa irin wannan hukumar ba.
A wani taron tuntubar da aka yi a Yola, Jahar Adamawa, Sanata Abdul’aziz Murtala Nyako mai wakiltar Adamawa Ta Tsakiya y ace idan aka kafa hukumar ta sake farfado da yankin arewa maso gabas, za ta ba da karfi wajen ganin an farfado da abubuwan more rayuwa da gina kasa da kuma ayyukan yi. Y ace su ‘yan Majalisar Dattawan arewa maso gabas sun yi taro sun cimma matsaya ta ganin an kafa wannan hukumar. Y ace arewa na bukatar sake ginuwa ne saboda tsananin barnar da aka yi.
A halin da ake ciki kuma, wasu masana na gargadin cewa za a shiga matsalar abinci sosai a arewacin Najeriya – musamman ma arewa maso gabashin Najeriya – saboda cikas din da Boko Haram ta haddasa ga manoma. Wani masani a harkar noma da muhalli mai suna Joseph Jarum y ace muddun ba a dau matakin da ya dace ba to za a shiga rigima saboda hare-haren bama-bamai da sauran nau’ukan tashe-tashen hankula sun hana manoma noma. Y ace dama akwai matsalar rashin ruwa, da rashin kulawa da bangaren noma. Don haka ya yi kira ga gwamnonin arewacin Najeriya da sub a da fannin noma irin kulawar da ta dace da shi.