To sai dai da alamun wadannan al-ummomin yanzu haka ana fama da matsaloli da dama. Domin bayan muhallansu da aka lalata, da rashin asibitoci, da makarantu da kuma gadojin da aka dasa wa nakiyoyi, wata matsala da al-ummomin yankin ke fuskanta a yanzu itace ta rashin abinci, yayin da wasu ke tsoron fara aikin gona, duk da cewa damina na kankama.
Wani mazaunin yankin wanda ya so a sakaye sunanshi cewa yayi “ka san cewa wannan abun da tsoro ne, domin sun daddasa nakiyoyi cikin wadannan gonaki, kuma in ka shiga gonarka sai ka je ka ga gawa. Zaka ga kasusuwa ya rube wanda ba’a binne ba. Kuma irin wannan akwai hatsari.
Da yake karin haske, wani masani a harkar noma Alhaji Musa Yakubu yayi gargadin cewa “kaga kwanakin baya ta wajen Maiha da sauransu an samu bom ya fashe. To irin wadannan abubuwan jama’a da yawa suna tsoro. Kuma wani lokaci kana tafiya a cikin daji ka ga bindiga, kaga gawar da ta lalace”.
To sai dai kuma ita sabuwar gwamnatin jihar Adamawan ta sha alwashin magance wadannan matsaloli da al-ummomin ke fuskanta.