Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawancin Yan Siyasan Najeriya Basu Da Gaskiya Inji Dr Usman Mohammed


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Dr Usman Mohammed yayi tsokaci game da zaben shugabanin majiisar dokokin Najeriya, yana mai cewa ‘’To da wahala yaki ci yaki cinyewa saboda an tara yan siyasa da yawa a wurin nan wanda kusan rabin su basu da gaskiya idanka tuna yadda akayi wannan zaben dattawan anyi wa wasu shige ne da kudundune akayi sauri aka nada wanda ake so saboda ana ganin kamar shi Lawal zai samu kuma da daurin gindin David Mark domin shi baya son Akume ya samu karfi da kassashi a cikin majilisar’’

Dr ganin cewa shi wannan sabon shugaba ba a dade da kammala wadannan zabubukan ba ya fito yace yabi kundin tsarin mulki sabo da haka ya amince da wannan zabe da akayi, me yasa yan majilisa zasu su dai wannan abin har yanzu basu gamsu dashi ba?.

‘’Yan majilisa dole suci gashin kansu shi bangaren zartarwa na shugaban kasa bangare ne daban yadda ce ba zaisa baki ba har aka kai ganan to lallai abubuwa sun tabarbare kuma sannan ita jamiyyar APC ta Makara kafin tace zata gyara wannan al’amari’’

Ganin cewa demokaradiyya ake yi a wannan majilisa kuma zaben da akayi shima demokaradiyya yan majilisa masu rinjaye Saraki suka zaba tunda masu rinjaye sune suke majilisa lokacin da akayi wannan zaben?

‘’A to sunce 57 to cikin 57 din nan nawa ne yan APC? me yasa ba a bar yan APC din ba kusan 50 ko kuma 47 da suke can ko kuma 47 ko 51 da suke can suna ganawa da Buhari su shigo majilisar su taru da yan uwansu kusan nawa kusan arbain da wani abu ne yan majilisar PDP a cikin wannan zabe’’

Amma da suna nan ai duk da haka ba zasu samu rinjaye ba?

‘’To a bar su su zauna mana su zabi wanda suke so a gani me yasa akayi hanzari aka yi shiga da kudundune’’.

Yanzu yadda su yan majilisar dattawa din da kuma shugabannin jamiyyar APC yadda suke fuskanta wannan lamari suna yin sa yadda yakamata?

‘’Bai kamata ba yakamata duk su jawo yan uwan su, su yan APC dukkan manbobin su, duka, idan sunga zasu yi wa shugaban Mubayia suyi mashi su bishi sannan su hakura suyi kasa aiki su sa kasa gaba’’.

To kaga a jamiyyar wakilai ma ba wabda jamiyyar APC take so ba Femi Gbajabiamila ba shi aka zaba ba, Yakubu Dogara aka zaba ba amma shi me yasa wannan bai tada kura ba?.

‘’To saboda su duk yan majilisar wakilai suna wurin suna so basa so sunyi zaben nan kuma anga cewa mafi rinjaye da suka yi zaben nan Dogara suka zaba’’.

Bello Habeeb Galadanchi ne yayi wannan hirar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:33 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG