Mutane da dama sun bayyana albarkacin bakinsu bisa da kamun da hukumomin Ingila suka yiwa tsohuwar ministar suka kuma gurfanar da ita gaban kotun kasar.
Masu sharhi da bada shawara sun yi hakan ne a kafofin labarai irin su gidajen talibijan da radiyo.
A wani rahoto da ta buga jaridar News Telegraph tace 'yan kwangila da sauran 'yan kasuwa da suke da alaka da tsohuwar ministar sun fara kona duk wasu takardu ko kuma wasu shaidu dake alakantasu da tsohuwar ministar domin gujewa bincike..
Wani yace matakin da gwamnatin Ingila ta dauka akan ministar ya faranta masa rai. Yace matakin kamata ya yi a ce gwamnatin Najeriya ce ta dauka. Talakawan Najeriya sun ji dadin abun da ya faru a Ingila da Alison Madueke.
Wani Mr. Jide Omokioro na cikin mutane hudun da suka gurfana gaban kotu a Ingila. Dama yana cikin wadanda tsohon gwamnan babban Bankin Najeriya ya zarga da cewa an yi anfani da kamfaninsa wajen batar da wasu makudan kudaden man fetur da kuma na kananzir.
Ofishinsa dake Ikoyi Legas yanzu wayas yake. To saidai jami'an EFCC sun gudanar da bincike a ofishin na Mr. Omokoro da gidajen Madueke da wasu ma da ake zargi da suke da gidaje a Legas.
Ga rahoton Babangida Jibril.
Your browser doesn’t support HTML5