Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Rage Farashin Man Fetur


Ministar Man Fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke
Ministar Man Fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke

Ministar ma'aikatar man fetur ta Najeriya Diezani Alison Madueke ta sanar da rage farashin man fetur

A bisa tanadin dokar man fetur ministar tace hakinta ne ta sanar da samun rage farashin litar mai da nera goma, wato daga nera casa'in da bakwai zuwa tamanin da bakwai.

Rage farashin ya soma ne daga daren jiya Lahadi.Dama can gwamnatin Jonathan ce ta kara kudin man daga nera 65 zuwa 97. Ministar tace ta umurci hukumar dake kula da farashin man fetur da ta tabbatar an bi sabon farashin sau da kafa domin anfanin duk 'yan Najeriya.

Ragewar ba zai rasa nasaba da faduwar farashen gangar mai a kasuwar duniya ba inda ya fadi daga dala 65 zuwa 45.

Shugaban kwamitin sufuri na majalisar wakilai Musa Sarkin Adar yace ragin har yanzu bai wadatar ba. Farashen kasuwar duniya ya fadi da kashi hamsin sabili da haka kamata yayi gwamnati ta rage farashinta da kashi hamsin ba nera goma ba kawai. Bai kamata farashin ya wuce nera 45 kowace lita.

Ga rahotoon Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG