Yayin da gwamnatin Najeriya ta bayyana a hukumance cewa ta samu rahoton kama tsohuwar ministan mai Diezani Alison-Madueke a birnin London inda daga baya aka sake ta, kungiyoyon fararen hula sun fara kalubalantar kotunan kasar kan yin adalci a yaki da cin hanci da rashawa.
A cewar Malam Awwal Musa Rafsanjani na kungiyar Transparency International da ke yaki da cin hanci da rashawa, bai kamata Najeriya ta rinka dogaro da kotunan kasashen waje fiye da na kasar ba wajen yaki da wannan matsala.
Ya kuma yi tir da yadda wasu da ake zargi ke garzayawa zuwa kotu domin su nemi mafakar kada a tuhume su.
“Muna Allah wadai da irin yadda wadanda suka ci amanar kasa su ke zuwa kotu domin su nemi damar a basu kariya ko kuma kada a tuhume su, ko kuma kada a ce su dawo da kudaden da suka sata, muna Allah wadai da irin wannan dama da kotu ke bayarwa.” In ji Darektan kungiyar, Rafsanjani.
A cewar Rafsanjani, abin kunya ne a ce wata kotun Najeriya ta wanke wani daga tuhumar aikata almundahana, sannan sai kuma wata kotu a kasar waje ta samu mutumin da laifi.
“Abin kunya ne misali, a ce James Ibori kotun Najeriya ta wanke shi kan cewa ba shi da hanu a sace-sacen da ake zargin shi da yi. Amma kuma sai ga wata kotu a Ingila ta same shi da laifi.”