Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Rage Kudin Mai Zai Yi Tasiri Kuwa


Ministar Man Fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke
Ministar Man Fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke

Biyo bayan rage kudin man fetur da gwamnatin Najeriya tayi daga ranar Lahadin da ta gabata wayancin gidajen man kasar sun rufe yayin da masu sayar da man ta bayan fagge ke cin karensu ba babbaka.

Yanzu dai ko a ga gidajen mai a rufe ko kuma a ga dogayen layi a gidajen da suka bude. To saidai matasa 'yan bakar kasuwa ko kasuwar bayan fagge suna sayar da man da dan karen tsada.

Wakilin Muryar Amurak Sale Shehu Ashaka ya zaga birnin Abuja inda yace rage kudin bai yi wani tasiri ba saboda mafi yawan gidajen man sun rufe. Wadanda aka zanta dasu sun ce man fa da tsada suka saya kuma ba zasu sayar da asara ba. Kuma injisu har yanzu ba'a rubuta masu cewa an rage kudin ba.

A can Sokoto kuma babu wani abun da ya sauya kamar yadda wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna ya shaida. Yace mutane sun san rage kudin man ba domin Allah aka yi ba domin farashen man ya riga ya fadi a kasuwar duniya. A garin na Sokoto babu wani da ya nuna wata murna domin an rage kudin mai. Mutane suna cewa idan gwamnati na son farantawa jama'a rai da an mayarda farashin daidai yadda shugaba 'Yar'Addu'a ya kayyade. Yin haka ne kawai zai sa 'yan Najeriya su dan yi murna.

A Bauchi jama'a sun yiwa ragin fasarar siyasa ne. Wakilinmu Abdulwahab Muhammad yace da ya nemi ra'ayin wasu akan ragin sai suka ce idan ma an yi ne domin a jawo ra'ayinsu su zabi Jonathan babu ba zasu yi ba. Wani ma cewa yayi koda an mayarda frashin nera biyar ba zai zabi Jonathan ba.

Ko a Ibadan jihar Oyo tunanen bai sauya ba. Wakilinmu Hassan Umar Tambuwal yace wasu na cewa siyasa ce kawai. Wasu sun ce ragewar bai damesu ba idan ana nufin su jefawa gwamnatin yanzu kuri'a ne a zabe mai zuwa. Ko a rage ko a kara ko a barshi yadda yake yanzu babu ruwansu da gwamnatin Jonathan. Akwai inda suka sa gaba.

A jihohi dake fama da kalubalen tsaro zai yi wuyi su ji tasirin ragin cikin kankanin lokaci. Wakilinmu Haruna Dauda Biu yace rage kudin bashi da wani tasiri a Maiduguri. Maimakon hakan ma lamarin ya haifar da karancin mai a cikin gari.

SAUTI: Shin Rage Kudin Mai Zai Yi Tasiri Kuwa - 3' 35" http://bit.ly/1ukeYOJ

HOTO: Diezani Alison Madueke, Ministar Man Fetur ta Najeriya

#Hausa #Nigeria

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG