Da yawa daga cikin wadanda ya zanta dasu sun bayyana cewa laifin daga mahukuntan kasar ne saboda basa adalci wajen tafiyar da al’amuran da suka shafi kyautatawa jama’a.
Wasu daga cikin wadanda ya zanta dasu, sun koka kan yadda masu gidajen mai suke kara farashin mai zuwa Naira 120 kan ko wani lita. A wasu wuraren sayar da ma farashin yana fin haka.
Idan za’a iya tunawa cikin makon jiya lokacinda aka fara fuskantar wannan matsala, jami’ai daga kamfanin hada hadar man fetur ta Najeriya NNPC, sunyi alkawarin cewa zuwa karshen makon jiya za’a daina fuskanatar wannan matsala.
A cikin ‘yan kwanakin nan ne ma ministar harkokin mai ta Najeriya Allison Madueke, ta ziyaci wasu gidajen mai inda ta yi zargin cewa dillalan mai ne suke haddasa karancin mai.