Ra’ayoyin ‘Yan Najeriya Kan Matsayin 'Yan Bindiga

'Yan Bindiga

Matasa a shafukan sada zumunta na ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da matakin halaka duk dan bindigar da aka kama da laifin kashe-kashe da satar mutane domin karban kudin fansa, inda wasu ke maraba da hakan wasu kuma na kushewa.

Tun bayan hukuncin kotun taraya mai zama a birnin Abuja da ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, wasu 'yan Najeriya musamman daga arewacin kasar da ke fama da kalubalen tsaro, suke cewa wanda ke kashe mutane da ba su ji ba su gani ba, bai cancanci a bar shi da rai ba.

Zainab Tanko Yakasai, ta bayyana cewa "kamata yayi duk wani dan bindiga da aka kama, a tatsi bayanan sirri a bakin sa saannan a yi masa abin da ya ke yi wa al’umma da ya ke kashewa ba tare da an yi masa laifin komai ba."

A wani bangare kuwa kyaftin Ibrahim Shariff, ya ce bai kamata ma a ayyana yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda ba, duba da yadda su ke ci gaba da aikata ta’adi ya na mai ba da shawarar cewa a kara neman wasu hanyoyin yin sulhu da su don samar da mafita mai dorewa.

Wata fitacciya a shafin Instagram Zahra Abdullahi, ta ce zancen yin sulhu da masu kashe mutane baya ga karban kudin fansa ba bu gaira ba dalili bai ma taso ba.

Ta kara da cewa sam ba su cancanci a yi zaman sulhu da su ba sakamakon mummunan yanayi da suke sanyan dubban jama’a.

Masana tsaro dai na ci gaba da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar tsaro ta hanyoyi daban-daban ciki har da masanin tsaro, Kabir Adamu wanda ya ce dole ne a rika hukunta masu aikata laifi kamar 'yan bindiga don ya zama darasi ga duk wanda ke da niyyar aikata duk wani irin na’uin laifi .

Kabiru Adamu ya ce ya kamata gwamnatoci a duk matakai su kara hobbasa wajen iko da dazukan arewacin kasar don korar yan bindigar daga ciki.

A baya-bayan nan ma sai da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta karbi tubar ’yan bindiga ba sai dai kashe su, domin a ganinsa, dan bindigar da aka kashe kawai shi ne ya tuba don zai je ya fuskanci ubangijinsa.

Tun farkon batun yin sulhu da yan bindgar ba’a taba jin gwamnatin tarayya ta shiga maganar ba.

Har yanzu dai yan bindigar na ci gaba da kashe-kashen mutane musamman a yankin arewa maso yamma da tsakiya, da saka haraji ga mutanen karkara, lamarin da ke saka al’ummar yankin cikin zaman dar-dar kusan kullum.