Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Dora Tarar Sama Da Naira Miliyan 1 A Jihar Zamfara; Al'umma Na Cikin Dar-Dar


Gunmen
Gunmen

Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewa ‘yan bindiga sun nemi sama da naira miliyan daya a matsayin haraji daga al’ummomi daban-daban a kananan hukumomin Zurmi, Kaura Namoda da Birnin Magaji a Jihar ta Zamfara.

Garurruwan da ‘yan bindigar suka nemi harajin daga gare su sun hada da Birnin Tsaba, Gabaken Mesa, Gabaken Dan-Maliki, Turawa, Askawa da Yanbuki kamar yadda gidan talabijan na Channels ta ruwaito.

Wani mazaunin daya daga cikin garurruwan da yan bindigar suka dorawa biyan harajin da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa mutanen Askawa sun biya Naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa don sako wasu mutane 18 da aka sace a baya da kuma kariya don hana kai hare-hare kan al’ummarsu.

Wata majiya ma ta bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da yan bindigar suke dorawa al’ummar yankin biyan haraji ba, ta na mai cewa tuni mutanen garurruwan suka fara tserewa daga yankunan da yan bindigar suka kaiwa sakon biyan haraji.

Rahotanni sun yi nuni da cewa sama da mutane dubu 10 na garurruwan Birnin Tsaba, Gabaken Mesa, Gabaken Dan-Maliki, Turawa, Askawa da Yanbuki suka tsere daga gidajen su zuwa makwabtan jihohin don neman mafaka.

Wasu kuma sun fantsama zuwa Abuja don tattaro harajin da aka saka al’ummarsu don kare su daga hare-haren ‘yan bindigar kaman yadda wakilinmu a jihar ta Zamfara ya shaida mana.

Haka kuma, rahotanni sun yi nuni da cewa ya zuwa yanzu wasu al’ummomi sun kasa tara kudaden kafin wa'adin ranar 11 ga watan Disamba da ‘yan bindigar suka bayar, lamarin da ke ci gaba da haifar da zaman dar-dar a yankunan da lamarin ya shafa.

A cewar wata majiya, garin Gabaken Mesa ya biya naira miliyan 1, Gabaken Dan-Maliki Naira miliyan 1 da Birnin Tsaba Naira miliyan 1, amma biyan wadannan kudadde ba su cika sharuddan adadin kudin da yan bindigar suka saka ba.

Majiyar ta kara da cewa "al’ummar garin ba su da karfin gwiwar kai labarin yanayin wajen jami’an tsaro, saboda a baya sun sha kai labari kuma ba bu matakan tsaro da aka dauka.

A nashi bangaren, kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya tabbatar da labarin na dorawa al’umma haraji da yan bindigar suka yi, yana mai tabbatarwa al’umma cewa gwamnati na aiki da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a yankunan.

Masanin tsaro Kabir Adamu dai ya ce wasu daga cikin hanyoyin da kan iya taimakawa waren yakar yan bindigar su ne samar da tsaro a dazukan arewacin kasar baki daya ta hangar mamaye su da hukunta mai laifi cikin gaggawa, da kuma karin horo ga jami’an tsaron kasar.

XS
SM
MD
LG