Putin Ya Sake Barazanar Amfani Da Makaman Nukiliya Kan Kasashen Yammacin Duniya

Shugaban kasar Russia Vladimir Putin

Shugaba Vladimir Putin ya gargadi Amurka da kawayenta akan cewar Moscow na duba yiyuwar maida martani da makaman nukiliya matukar suka bari Ukraine ta kai hari cikin Rasha ta hanyar amfani da makamai masu linzami masu cin dogon zango da aka kera a kasashen yammacin duniya

A gargadin baya-bayan nan daga jerin wadanda ya yi a baya, a jiya Laraba, Putin ya kara zayyano jerin dalilan da zasu sabbaba Rasha yin amfani da makaman nukiliya.

Russia

A cewarsa, haka za ta iya kasancewa, wajen maida martani ga wani babban harin da aka kawo cikin Rasha daga ketare ta hanyar amfani da jiragen saman yaki ko makami mai linzami ko jirgi marasa matuki.

“Zamu zartar da hukuncin bai daya kan duk kasar dake da makamin nukiliya kuma take gaba da Rasha da ta taimaka wajen kai mana farmaki” a cewar Putin.

Idan har Putin ba da gaske yake yi ba, kamar yadda Ukraine da wasu magoya bayanta suka zata, to lokaci yayi da kasashen yamma zasu kara yawan taimakon sojin da suke baiwa Kyiv ba tare da la’akari da barazanar dake fitowa daga Moscow ba.

Idan har hakan ta kasance da gaske, to akwai hatsari-kamar yadda Moscow ta sha nanatawa kuma Washington ta shaida hakan-yakin na iya rikidewa zuwa yakin duniya na uku.

-Reuters