Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun ICC Ta Ba Da Izinin Kama Putin


TSOHON HOTO: Shugaban Rasha Vladimir Putin
TSOHON HOTO: Shugaban Rasha Vladimir Putin

Kotun har ila yau ta ba da izinin kama kwamishiniyar kare hakkin yara a ofishin shugaban kasar ta Rasha, Maria Alekseyevna Lvova Belova, wacce ita ma ake zargin ta da hannu a lamarin.

A yau Juma’a kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta ba da umurnin a kama shugaban Rasha Vladimir Putin saboda laifukan yaki da ake zargin ya aikata, wadanda suka hada da yin garkuwa da kananan yara a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, kotun ta ICC ta zargi Putin da laifin “kwashe wasu yara kanana daga yankunan da Rashar ta karbe iko a Ukraine ba bisa ka’ida ba, inda aka mayar da su Rasha.”

Kotun har ila yau ta ba da iznin kama kwamishiniyar kare hakkin yara a ofishin shugaban kasar ta Rasha, Maria Alekseyevna Lvova Belova, wacce ita ma ake zargin ta da hannu a lamarin.

Sai dai ana ganin gurfanar da wani dan kasar Rasha a gaban kotun ta ICC, wani abu ne da zai zama mai kamar wuya, duba da cewa Rashar ba ta mika ‘yan kasarta don su fuskanci hukunci a wata kasa.

A jiya Alhamis wani bincike da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ya ayyana hare-haren da Rasha ke kai wa kan Ukraine a matsayin wadanda wadanda za a iya kallon su a matsayin laifukan yaki.

A ranar 24 ga watan Fabrairun 2022, dakarun Rasha suka fadawa Ukraine da yakin da kasashen duniya da dama suke Allah wadai da shi.

Daruruwan dubban mutane sun mutu tun bayan fara yakin yayin da aka tafka asarar dukiyoyi da dama.

XS
SM
MD
LG