PM David Cameron Ya Katse Hutunsa Kan Tarzoma A London

'yansanda kwantarda tarzoma a Ingila suke kokarin shawo kan tarzomar.

PM Ingila David Cameron zai takaita hutu da yake yi a italiya, ya hanzarta komawa London domin ya tunkari zanga zanga mafi muni da birnin ya gani cikin shekaru masu yawa.

PM Ingila David Cameron zai takaita hutu da yake yi a italiya, ya hanzarta komawa London domin ya tunkari zanga zanga mafi muni da birnin ya gani cikin shekaru masu yawa.

An kona gine gine motoci da kuma wuraren daukan fasinja kan tituna, yansand a sun kara da matsa a dare na uku a jere jiya litinin unguwanni birnin London masu yawa. Masu kwasar ganima sun kai hari kan wuraren cin abinci da kantuna, san nan suka kai wa ‘Yansanda hari da kalabe da mai da aka cunna musu wuta.

Wan nan tarozmar ta biyo bayan harbe da wani mutum da shekaru 29 da haifuwa, a unguwar marasa karfi ta Tottenham dake binrin London a karshen makon jiya. Zanga zangar lumana da aka fara ranar Asabar domin kisan, ta rikada ta zama tarzoma ranar Asabar, lokacind a masu zanga zangar suka fara jifan ‘Yansanda da duwatsu,suka fasa tagogi da kona motocin shiga dana haya.

‘Yansanda sun bada labarin sun kama mutane 215 zuwa yanzu. ‘Yansanda 35 sun jikkata,ciki har da ‘Yansanda uku da mota ta taka su lokacinda suke kokarin kama wadanda suke zargi da aikata laifi.

Mukaddashin PM Nick Clegg yace tarzomar bata da tushe, kuma gwamnati ba zata amince da haka ba. Sakatariyar harkokin cikin gida Theresa May ta yi Allah wadai da masu zaga zanga, wadanda ta kira masu laifi.

Amma mazauna binrin London sun ce zanga zangar ta samo asali ne kan fusatar jama’a sabili da mummunar yanayin tattalin arziki a arewacin London, da suka hada har da yawan mutane da basu da aikin yi, da kuma rage tallafi da gwamnati take bayarwa.