Hukumar zaben tace Dr. Shehu Zabayi Nuhu ya samu kuri'u 92,056 yayin da Barrister David Umar na jam'iyyar APC ya tashi da kuri'u 87,405.
Amma dan takarar jam'iyyar APC Barrister David Umar yayi watsi da sakamakon domin wai jam'iyyar PDP tayi anfani da karfi da kuma zunzurutun kudi da ta sayi kuri'un jama'a a lokacin zaben. Yace bai amince da sakamakon ba domin bai fito sanadiyar yin zabe mai adalci ba. Yace duk mazabun da ya je ya ga ana sayen kuri'u.
A nashi gefen bayan ya karbi takardar lashe zaben, Dr. Nuhu yayi magana da manema labarai inda ya bayyana nasarar da ya samu cewa daga Allah ta ke. Daga bisani ya nemi hadin kan 'yan adawa domin kasa ta ci gaba. Yace shi bai san dalilin korafin da 'yan adawa suke yi ba domin a kowace mazaba duk wakilan sun sa hannu sun amince da sakamakon.
Ita ma jam'iyyar PDP ta musanta zargin cewa tayi anfani da tsabar kudi domin sayen kuri'un jama'a. Alhaji Hassan Saba jami'in yada labarai na jam'iyyar yace batun duk kage ne na 'yan adawa. Idan sun kamasu suna anfani da kudi ai suna da hanyar da zasu gayawa jama'a su kuma nemi hakinsu.
An kwashe makonni biyu ana zaben sakamakon matsalolin da aka samu a wasu mazabu na kananan hukumomi shida daga cikin tara dake yankin. Kujerar da suka yi takara akai ita ce Sanata Dahiru Kuta ya mutu ya bari watanni uku da suka gabata.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Your browser doesn’t support HTML5