Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC ta Kddamar da Shugabanninta na Arewa Maso Yamma


APC
APC

Shugaban jam'iyyar APC na kasa ya jagoranci bikin kaddamar da shugabannin jama'iyyar na arewa maso yamma a Sokoto.

An yi wannan taron kaddamarwan ne a Sokoto fadar gwamnatin jihar.

Taron ya hada masu ruwa da tsaki a yankin yammacin kasar har ma da sassan Najeriya da gwamnonin wasu jihohin Najeriya dake karkashin jam'iyyar.

Kusan yawancin shugabannin jam'iyyar sun samu halartar taron in banda Janaral Buhari da Sanata Bola Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasar Nageriya Alhaji Atiku Abubakar.

A jawabinsa gwamnan jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya maida hankali ne akan wasu gwamnonin PDP da yace suna sha'awar shiga APC. Gwamnoni ne da suke tattaunawa tare dasu yayin da suke cikin jam'iyyar PDP. Yace sun yadda zamansu a cikin PDP ba alheri ba ne. Yace su suna cikn APC cikin jin dadi da 'yanci. Yace amma su can har yanzu bata sake zani ba.

Taron ya baza kolin daruruwan 'yan takara a hotuna da alluna daban daban da suka yi tarayya wajen takarar mukami daban daban.

Saidai gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar yace yawan 'yan takarar ba matsala ba ce. Duk wanda ya shiga neman kujerar shugaban kasa ko ta gwamna ko wani matsayi ya san cewa mutum guda ne za'a tsayar. Duk wani zaton cewa APC zata samu matsala wajen tsayar da dan takara tunani ne na 'yan adawa. An yi irin wannan tunanen lokacin fitar da shugabannin jama'ar na kasa amma Allah bai kawo matsala ba.

Amma yayin da take mayar da martani jami'iyyar PDP reshen jihar Sokoto tace ko ta ji a jikinta. Babban abun da ya dameta game da taron shi ne yin anfani da kudin jihar domin karbar bakuncin taron. Alhaji Ibrahim Milgoma shugaban PDP na jihar Sokoto yace kudaden bai kamata a kashesu akan taron ba. Mutane na cikin wani mawuyacin hali suna neman taimako ga 'yan kwangila da ba'a biyasu ba. Lokacin da suka yi taron Abuja gwamnan jihar Sokoto ya dauki nauyin, ga kuma wannan taron yanki.

Shi gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko yace zargin baya kan hanya. Yace ba kudin gwamnati suka yi anfani dashi ba. Idan ma haka ne ita tashar talibijan dake Sokoto ta gwamantin tarayya bata tallar komi sai shugaba Goodluck Jonathan.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG