Magoya bayan masu neman shugabancin shugaban majilisar dattawa dana wakilai na shigowa cikin Abuja domin shedawa wannan zaben da za a yi zauren majilisun baya ga yan takaran jamiyyar APC sanata Ahmed Lawal a majilisar dattawa da Femi Gbajabiamila a wakilai magoya bayan masu adawa da matsayin na karfafa wa gwanayen nasu gwiwa na nuna barin zaben shine zai karfafa demokaradiyya.
‘ Yakubu Aliyu na tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Das a jihar Bauci yace idan an kada Dogara mun tabbatar an kada shi ne zamu dauki kaddara.
Tsoffin gwamnoni da wadanda suka shiga a waren PDP da suka shiga gamayyar APC na mara baya ga Bukola Saraki don jagorantar maalisar dattawa, a kaikaice dai suna zargin uban jamiyyar Bola Tinubu nason nada mukarabban sa ne a manyan mukamai ga dai abinda Tsohon Gwamnan Zamfara Ahmed Sani yana mai cewa,
‘’Tunda ana son a tilasta kana ji shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari ya fito karara yace wa duniya baida ra'ayi baida sha'awa ga wani dan takarar sa, me yasa yayi haka domin yaji ana yawo da sunan sa ana cewa ga wanda yake so ga wanda baya so, su kuma wadannan da suke kokarin yin hakan kowa yasan su duk Najeriya na tabbata insha Allahu an san su dama haka suka saba siyasa saboda haka muke son mu nuna musu cewa siyasa ta canja jamiyyar APC jamiyya ce ta al’umma baki daya ta Najeriya kuma insha ALLAHU ALLAH yafi sanin zukatan mu gurin mu shine muga cewa mun taimakawa wannan bawan ALLAH ya sauke nauyin da ALLAH ya dora mashi, kuma mu kanmu ALLAH zai tambaye mu’’