Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Fara Kokawa da Sabuwar Gwamnati


Matasa sun taru suna wakoki
Matasa sun taru suna wakoki

Ranar 29 ga watan da ya gabata ne aka rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya.

Mako daya bayan rantsar da shugaba Mohammadu buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya, matasa sun fara korafi akan tafiyar gwamnatin. Matasa dai sun taka muhimmiyar rawa a babban zabukan da aka gudanar a Najeriya.

Shugaban wata kungiyar matasa mai zaman kanta mai suna Youth Global Mission, kwamred Abdulhamid Sa'ad, ya koka game da yadda kawo yanzu sabuwar gwamnati bata fara damawa yadda ya kamata da matasa ba.

A cewar Kwamred Abdulhamid, abubuwan dake faruwa a matakai da bam da bam na nuna cewa ba a damawa da matasa, saboda a lokacin da aka kafa kwamitin mika mulki ga sabuwar gwamnati akwai karancin wakilcin matasa. Bayan haka a lokacin kemfe, akwai bukatu da suka hada da samar wa matasa da ayyukanyi da kuma tabbatar da tsaro a kasa da sabon shugaban kasa da jam'iyyarsa suka ce zasu maida hankali akai.

Kwamred Abdulhamid ya kara da cewa, dole ne a matsayinsu na shugabannan matasa su mika kokensu ga gwamnatoci tun daga matakin gwamnatin tarayya zuwa da kananan hukumomi don a tuna da bukatocin matasa kafin a gama nada-naden mukamai.

Ga Baraka Bashir da rahoton

XS
SM
MD
LG