A yayin da ake shirin buga wasan karshe na lashe kofin zakarun kulob kulob na Turai asabar din nan a birnin Berlin, ta yaya sauran kungiyoyi biyu da suka rage, Juventus da FC Barcelona suka kawo wannan gaba daga cikin kungiyoyi 77 da suka nemi wannan kambin?
Ita dai Juventus ita ce ta bada mamaki ganin kawowarta wasan karshe. A zagayen farko, ta sha kashi a hannun Atletico Madrid da Olympiakos, amma ta samu tsallakewa zuwa zagaye na biyu a matsayin ta biyu a wannan rukuni, a bayan kungiyar Atletico Madrid. A zagayen kwaf daya kuwa, Juventus ta fara nuna bajimta inda ta cire sanannun kungiyoyi irinsu Borussia Dortmund, Monaco da Real Madrid.
Ita kuwa FC Barcelona ta nuna bajimta a duk tsawon wannan gasa ta bana. Ita ce ta daya a rukuninta. A zagayen kwaf daya kuwa, ta doke Manchester City, da wasu kungiyoyi biyu da aka sa ma ran lashe kofin nan tun farko, PSG da Bayern Munich.
Hausawa suka ce baa san maci tuwo ba sai miya ta kare. Har yanzu babu wanda zai iya ce tabbas ga wanda zai lashe kofin nan gobe asabar, koda yake an fi maida karfi a kan FC Barcelona, musamman a saboda kasancewarta tana da Lionel Messi, Luis Suarez da Neymar. Amma ita ma Juventus, ba kanwar lasa ba ce.