Makarantu a lardin Luoyang na kasar China sun yanke shawarar anfani da wata sabuwar fasaha da suka kirkiro domin magance matsalar satar amsa da wasu dalibai kanyi a yayin da suke rubuta jarabawa.
Makarantun sun gano cewar akasarin hanyar da dalibai ke anfani da ita wajan satar amsa ita ce wayar salula ko wayar tafi da gidan ka da sauran kananan na’urori makamantan su.
A sakamakon haka ne duk lokacin da ‘yan makarantun suka shirya daukar wata jarabawa musamman irin wadda suke kwashe kwanaki biyu suna rubutawa, za su rika jin kugin wani abu daga wajen azuzuwan su wanda zai kasan ce wani dan jirgi ne mara matuki wanda zai rika shawagi a bisan gini ko azuzuwan da daliban ke zana jarabawar.
Wannan jirgi zai rika daukar rahotannin duk wani bayanin da mai zana jarabawa ya nema ta wayar salula a yayin da yake zana jarabawar ya kuma aikawa malaman da ke kula da masu zana jarabawar.
Jirgin mara matuki zai yi ta shawagi a saman gine ginen kuma yana iya sauka da kanshi. Wannan fasaha dai a cewar sakataren gidan radiyon Luoyang, Mr Zeng Ying Yong, kamar yadda kafar sadarawar Google ta fassara, "zata taimaka wajan kara wa yara jajircewa wajan neman ingantaccen ilimi da kuma dogaro da kai."
Dan haka ya kara da cewar duk waddanda ke aikata irin wannan hali na satar jarrabawa to su kuka da kansu, domin Kuwa babu yadda zasu iya satar amsa ba tare da wannan jirgi ya gano ba.