NNPLC Ta Yi Kira Ga Masu Zuba Jari A Mai, Iskar Gas Da Su Karkato Najeriya

Mele Kyari NNPCL

Mele Kyari NNPCL

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi kira ga masu zuba jari a duniya da su karkato da hankalinsu ga bangaren mai da iskar gas na Najeriya domin a halin yanzu al’ummar kasar ta zama matattarar masu saka hannun jari saboda sauye-sauye da aka yi da kuma tsare-tsare masu dacewa da masu zuba jari

Mataimakin Shugaban Kamfanin NNPC, Udy Ntia ne ya yi wannan kiran a ranar Talata yayin wani zama da masu zuba jari da aka gudanar a Houston, Texas, Amurka.

Da ya ke jawabi kan taken, “Spotlight” wato janyo hankalin zuba jari ga man fetur da iskar gas Ntia ya jaddada cewa, Najeriya ta kasance matsayin kasa mai kyau wajen zuba jari domin a halin yanzu al’ummar kasar na kara fadada masana’antunta na mai da iskar gas don biyan bukatar makamashin duniya da ake samu sakamakon tashe-tashen hankula na bangarorin yanki, da siyasa, da manufofin makamashi na gwamnatin Amurka.

"A gare mu a Najeriya, duk da matsalolin rashin tabbas kan makamashi a duniya, ciki har da na Turai, muna ganin dama mai mahimmanci.”

"Mun tsara dabarun mu don yin amfani da yanayin farashi mai karfi na yanzu, wanda ya kasance mai kyau a cikin shekaru biyu zuwa uku da suka gabata. A sakamakon haka, muna sa ran zuba jari mai yawa a fannin,” in ji shi.