Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Jinjinawa NNPCL Kan Sake Bude Matatar Man Warri


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jin dadinsa akan sake bude matatar mai ta Warri da kamfanin man kasar NNPCL ya yi.

Sanarwar da mashawarcin shugaban kasar na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar a yau Litinin, ta bayyana hakan da samun gagarumar nasara a 2024 wacce ta sake karfafa fatan da ‘yan Najeriya ke da shi a kan gwamnatinsa.

“A yau, matatar mai ta Warri ta koma bakin aiki makonni bayan da kamfanin NNPCL ya farfado da matatar Fatakwal a watan Nuwamban da ya gabata daka iya tace ganga 60, 000 a kowace rana.

“Da sake farfado da matatar Warri bayan shafe dimbin shekaru bata aiki, Shugaba Tinubu ya sake bayyana aniyar gwamnatinsa ta bunkasa tace mai a cikin gida tare da mayar da Najeriya cibiyar hada-hadar albarkatun mai a nahiyar Afirka.

Cikin kwarin gwiwa Shugaba Tinubu ya kara da cewa kasancewar matatar Warri daka iya tace ganga 125, 000 ta danyen mai a kowace rana ta koma bakin aiki a kan kaso 60 cikin 100, shirin gwamnatinsa na tabbatar da samu da wadatuwar makamashi na tafiya yadda ya kamata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG