Amma kungiyar ta ce, Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya fito ya bayyana inda kudaden suka sulale, tunda hakkin ƴan na kasa ne.
Kungiyar da ke fafutukar kare ƴancin ƴan kasa da ƙididdigar ayyuka ta (SERAP) ta yi kira ga kamfanin albarkatun man fetur ta Najeriya (NNPCL) da babban jami’in kamfanin, Mele Kyari, da su fito su yiwa ƴan kasar cikakken bayani kan bacewar Naira biliyan 825 da kuma dala biliyan 2.5 da aka ware domin gyaran matatun man kasar.
Ƙungiyar SERAP, ta ce bayanin bacewar wannan kudaden na daga cikin rahoton da babban jami’in bincike na kasar ya fitar, a ranar 27, ga watan Nuwamba 2024.
SERAP ta bukaci Mele Kyari da ya lalubo tare da mika mutanen da ke da hannu wajen karkatar da kudade ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ICPC.
SERAP, ta kara da cewa ire-iren wannan badaƙala na kudadena kassara cigaban tattalin arzikin kasar da kuma jefa ƴan kasar cikin mawuyacin hali.
Kungiyar ta SERAP, ta ce, ta ba wa kamfanin na NNPCL kwanaki 7, domin su fito su yiwa ƴan kasa bayani game da inda kuɗaɗen suke, ko kuma su fuskanci Shari’a.
Kabir Sa’idu Dakata, babban daraktan cibiyar wayar da kan al’umma akan shugabanci nagari da adalci wato KAJA, ya ce wannan yunkuri na kungiyar SERAP abu ne me kyau, kuma kamata ya yi hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa suna bibiyar irin wannan al’amari.
Imrana Wada Nas shugaban rundunar talakawan Najeriya, ya ce dama akwai ayar tambaya ga shugaban kamfanin na NNPCL, game da yadda yake tafiyar da kamfanin.
‘Yan kasar dai na cigaba da kokawa game da matsin rayuwa da suke fama da shi, biyo bayan cire tallafin man fetur da Gwamnatin kasar tayi.
Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna