Kamfanin mai na NNPCL a Najeriya, ya sanar da kulla wata yarjejeniya da wani bankin kasar Masar inda zai karbi rancen dala biliyan uku.
Sanarwar da kamfanin na NNPCL ya fitar a ranar Laraba ta nuna cewa a hedkwatar bankin da ke birnin Alkahira aka kulla wannan yarejejeniya.
Kudaden a cewar NNPCL za a yi amfani da su ne wajen biyan kudaden man da aka karbo bashi, amma kuma za su iya taimakawa wajen daidaita kasuwar canji.
“Sanya hannu a wannan yarjejeniya, wacce aka yi a yau (Laraba) a hedkwatar bankin da ke birnin Alkahira na Masar, za ta samar da kudaden gaggawa da kamfanin NNPCL zai tallafawa yunkurin da Gwamnatin Najeriya ke yi na samar da daidaito a kasuwar canji.” Sanarwar ta ce.
Farashin dala ya yi tashin da aka dade ba gani ba, inda ya kai har 950 a kasuwar bayan fage kafin daga baya ta dawo 790.
Hakan ya sa farashin kayayyakin musamman wadanda ake shiga da suka yi tashin gwauron zabi.
Sanarwar dai ba ta ambaci sharudda ko ka’idojin da aka kulla yarjejeniyar a kansu ba, kamar na iya tsawon lokacin da kamfanin na NNPCL zai kwashe yana biyan bashin.