Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Kashe Dala Biliyan 7.5 Kan Tallafin Man Fetur Zuwa Tsakiyar 2023 


Ministar Kudi a Najeriya Zainab Ahmed
Ministar Kudi a Najeriya Zainab Ahmed

Najeriya za ta ci gaba da ba da tallafin man fetur har zuwa tsakiyar shekarar 2023 sannan ta ware Naira tiriliyan 3.36 (dala biliyan 7.5) don wannan bukatar, ministar kudi Zainab Ahmed ta ce. 

WASHINGTON, D.C. - Najeriya, wacce ita ce kasar da ta fi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, ta kashe naira tiriliyan 2.91 kan tallafin mai a tsakanin watan Janairu zuwa Satumbar 2022, a cewar kamfanin man kasar na NNPC.

Hedikwatar NNPC
Hedikwatar NNPC

Hukumomin Najeriya sun jima suna korafin cewa wadannan kudade hana kasar samun walwalar gudanar da wasu ayyuka a sauran ma’aikatu.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2023 na Naira tiriliyan 21.83 a ranar Talata, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 49, bayan da ‘yan majalisa suka kara kasafin kudin da kashi 6.4% tare da kara hasashen farashin man fetur.

-Reuters

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG