Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Yi wa Rayuwata Barazana Saboda Sauyen-sauyen Da Mu Ke Yi A NNPC – Mele Kyari


Malam Mele Kyari
Malam Mele Kyari

Kyari ya ce sun yi nasarar rufe haramtattun matatun mai da dama tun da aka fara aiwatar da sauye-sauyen.

Shugaban kamfanin mai na NNPC Limited a Najeriya, Mele Kyari ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana saboda sabbin sauye-sauyen da suke aiwatarwa a kamfanin.

Kyari ya bayyana hakan ne yayin taron da wani kwamitin majalisar wakilain Najeriya ya gudanar a ranar Laraba a Abuja, kan yaki da cin hanci da rashawa.

“Ana yi wa rayuwata barazana, ina samun sakonnin barazana ga rayuwata da dama, amma hakan bai dame mu ba, mun yi amannar cewa, babu wanda zai mutu har sai idan lokacinsa ya yi.” In ji Kyari kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga NAN.

Kamfanin na NNPC na gudanar da sauye-sauye a fannonin daban-daban, lamarin da ya kai ga nasarar rufe wasu haramtattun matatun mai da ke aiki a boye.

A cewar Kyari, ire-ire wadannan haramtattun matatun man ne suke sa adadin man da ake fitarwa a kasar ya ragu da gangar mai dubu 700.

XS
SM
MD
LG