Nnamdi Kanu, Sunday Igboho Sun Maka Gwamnatin Najeriya A Kotu

  • Murtala Sanyinna

Zaman sauraren shari'ar Nnamdi Kanu a Babbar Kotun Tarayyar Najeriya a Abuja.

Jagoran Kungiyar IPOB mai neman ballewa a kudu maso gabashin Najeriya Nnamdi Kanu, da dan fafutukar kafa kasar Yarbawa a kudu maso yamma Sunday Igboho, sun shigar da karar gwamnatin Najeriya a gaban kotu, a yayin da gwamnatin ke kokarin hukunta su bisa zargin ta da zaune tsaye.

Lauyan Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar nan ta IPOB mai fafutukar kafa kasar Biyafara, Aloy Ejimakor, shi ne ya shigar da kara a gaban wata babbar kotun jihar Abia, a madadin Kanu.

Kanu na bukatar a biya shi diyya ta zunzurutun kudi har naira biliyan 5, sanadiyyar yanayin damuwa da rashin lafiyar da gwamnatin ta jefa shi a ciki.

Kanu ya shigar da kara ne akan gwamnatin tarayya, Ministan shari’a Abubakar Malami da babban hafsan sojin Najeriya Faruk Yahaya da wasu da dama, ciki har da babban sufeto Janar na ‘yan sanda da babban daraktan hukumar tsaron farin kaya ta SSS.

A cikin karar, Kanu ya bukaci kotu da ta ayyana kamo shi da aka yi daga kasar Kenya zuwa Najeriya a zaman ya saba doka, haka kuma a sake shi daga tsarewar da ake masa.

Nnamdi Kanu

Lauya Ejimakor ya kuma nemi a gaggauta maida Kanu a kasarsa da yake zama wato Birtaniya, domin jiran sakamakon duk wata bukata da gwamnatin Najeriya za ta iya nema daga hukumomin kasar Birtaniya, domin kamo shi a can.

Haka kuma ya nemi kotu da ta tilastawa gwamnatin tarayya ta bayar da takardar neman afuwa kan keta hakki da ‘yancin wanda yake wakilta.

Gwamnatin Najeriyar ta sami nasarar kama Nnamdi Kanu ne daga wata kasa, inda ta tiso keyarsa zuwa Najeriya, ta kuma gurfanar da shi a gaban kotu, bisa zarge-zargen cin amannar kasa, tunzura jama’a da ta da zaune tsaye, kazalika da haddasa kisan jama’a da dai sauransu.

A daya bangaren kuma, a ranar Talatar nan wata babbar kotun jihar Oyo ta ci gaba da sauraren karar da Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, ya gabatar mata.

Igboho yana karar Ministan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami, da shugabannin hukumar tsaro ta DSS a matakin kasa da kuma na jihar Oyo.

Sunday Igboho

Lauyan Igboho, Sunday Adeyemo ya shigar da karar ne yana neman kotu ta da dakatar da Ministan Shari’a da hukumar DSS daga kokarin kama shi ko cin zarafinsa, da kuma toshe asusun ajiyar sa na banki.

Kotun ta tsaida ranar jiya Talata domin yanke hukunci akan shari’ar, to amma kuma hakan bai samu ba, inda ta dage ba da hukuncin har zuwa ranar 17 ga wannan watan na Satumba, kazalika kuma ta tsawaita umarnin dakatar da daukar duk wani matakin Ministan shari’a da hukumar DSS akan Igboho, har ranar yanke hukunci.

Yanzu haka dai Igboho na zaman gudun hijira a kasar Jamhuriyar Benin, bayan ya sami arcewa sa'adda jami'an tsaro suka kai samame a gidansa, bisa zargin ayukan ta da zaune tsaye.