Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amnesty International Na Marawa 'Yan ta'adda - Gwamnatin Najeriya


Shugaba Buhari (Facebook/Min of Information)
Shugaba Buhari (Facebook/Min of Information)

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta zargi kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International da marawa ‘yan ta’adda baya, a maimakon dimbin jama’ar da suke cutarwa.

Gwamnatin ta Najeriya na mai da martani ne kan rahoton baya-bayan nan na hukumar kare hakkin bil adama ta Amnesty International, dangane da yanayin hakkin dan adam a Najeriya.

Rahoton kungiyar ta Amnesty International dai ya zargi jami’an tsaron Najeriya da cin zarafin masu sukar lamirin gwamnati, da kuma kisa da kama ‘yan kungiyar IPOB ba bisa ka’ida ba.

A wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Buhari kan sha’anin watsa labarai Garba Shehu ya fitar, gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa ba zata yi kasa a gwiwa ba, za ta ci gaba da kokarin yaki da ta’addanci ta kowace hanya.

A yayin da kuma take musanta rahoton na Amnesty International, gwamnatin ta Najeriya ta bayyana aikin kungiyar a matsayin kariya da kuma musamman karfafawa wadanda ke kalubalantar gwamnati ta hanyar tashin hankali.

“Kariyar ayukan Nnamdi Kanu da haramtacciyar kungiyar ta’addanci ta IPOB, aiki ne kawai na halatta ayukan su ga al’ummomin kasashen yammaci” in ji sanarwar ta gwamnati.

Gwamnatin ta kuma zargi kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biyafara wato IPOB, da cewa ta yi tanadin manyan makamai masu yawa da kuma bama-bamai, domin hare-haren da take kai wa ga jami’an tsaro da hukumomin gwamnati a fadin kasar.

Ta ci gaba da cewa “Kungiyar IPOB tana kisan ‘yan Najeriya, suna kisan jami’an ‘yan sanda da soji, suna kona gine-ginen gwamnati, to amma me ya sa su kungiyar ta Amnesty International ba ta magana.”

A kan haka ne gwamnatin ta yi zargin cewa kungiyar ta Amnesty International ta shiga dumu-dumu a cikin siyasar Najeriya.

Sanarwar ta ce bisa tanadin doka ma kungiyar ba ta da hurumi ko ‘yanci na kasancewa a Najeriya, tare da bayyana cewa gwamnati za ta bude bincike akan jami’an da ke ofisoshin kungiyar a Najeriya.

XS
SM
MD
LG