Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Sunday Igboho a Jamhuriyar Benin


Sunday Igboho.
Sunday Igboho.

An kama wani mai fada a ji na kungiyar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho a Cotonou da ke Jamhuriyar Benin.

Ko da yake, har yanzu jami'an tsaro a kasar ba su tabbatar da kamun ba, sanannen masanin tarihin kuma shugaban kungiyar Yarbawa ta Umbrella Body of Yoruba Self-Determination Groups, Farfesa Banji Akintoye, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya tabbatar da faruwar lamarin kamar yadda Channels ta ruwaito.

Akintoye ya ce "na samu labarin daren jiya da daddare cewar an kama Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho a filin jirgin saman Cotonou,"

A farkon watan nan hukumar tsaro ta DSS ta ayyana Igboho a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bayan wani samame da ta kai gidansa.

Karin bayani akan: Jamhuriyar Benin, Channels, DSS, Sunday Adeyemo, Sunday Igboho, The Punch, Cotonou, kasar Jamus, Nigeria, da Najeriya.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, jami'an tsaro a Jamhuriyar Benin sun cafke Igboho a filin jirgin sama na Cotonou a daren Litinin yayin da yake kokarin guduwa zuwa kasar Jamus.

“An kama shi ne a Cotonou yayin da yake kokarin fita waje a daren Litinin da nufin tafiya kasar Jamus. Ya kamata jami’an tsaro a Jamhuriyar Benin su dawo da shi Najeriya ranar Talata, ”in ji majiyar.

A lokacin da aka kai samame gidansa Sunday Igboho, hukumomin tsaro sun yi ikirarin samun tarin makamai da ya boye.

Hakan ya sa suka ayyana nemansa ruwa a jallo saboda makaman da aka samu, zargin da yake ta musantawa.

XS
SM
MD
LG