Wani babban jigo a yankin Kudu maso yammacin Najeriya Chief Gani Adams ya ce mafi akasarin hanyoyin da dan fafutukar kafa kasar Yarbawa Sunday Igboho ya ke bi sun kauce hanya.
A yayin da yake jawabi a wajen wani taron jama’a da aka yayata a kafafen sada zumunta na yanar gizo, Gani Adams ya ce Igboho yana saka farfaganda da ta wuce kima a daukacin hankoron da yake yi.
Gani Adams, wanda ke da babbar sarautar kasar Yarbawa ta ‘Aare Onakakanfo’, ya ce barazanar da dan fafutukar ya yi na bude iyakokin kasa da karfi ya saba ka’ida, haka kuma ikirarin da ya yi na cewa ko ‘yan sanda dubu suka kai samame a gidansa ba za su dawo da rai ba, shi ma bai dace ba.
“ka ce zaka bude kan iyakar kasa, wannan ai sai ya janyo yaki. Ba ka da ko makaman yaki amma kana takalar sojoji. Wannan sam ba za ta kai ka ko ina ba” Gani Adams ya fadawa Sunday Igboho.
Ya ci gaba da cewa “ka ce idan ‘yan sanda dubu suka je gidan ka ko dari daya ba za su dawo ba. Babu bukatar duk wannan farfagandar. Bai kamata farfaganda ta yi yawa a cikin fafutukar ballewa don kafa kasa ba.”
Karin bayani akan: Sunday Igboho, Gani Adams, DSS, Nigeria, da Najeriya.
Basaraken wanda shi ma tsohon da gwagwarmaya ne, ya bayyana rashin gamsuwa da yadda masu kiran kan su ‘yan gwagwarmaya suke bayyana wasu al’amura da ya kamata a sirranta su a kafafen sada zumunta na yanar gizo.
“Mafi akasarin Abubuwan da Sunday Igboho ya ke yi ba daidai ba ne. Na gaya masa hanyar da yake bi ba daidai take ba” in ji Gani Adams.
Haka kuma ya shawarci Sunday Igboho da ya gargadi mabiyansa akan Abubuwan da suke furtawa, domin kada su jefa shi a cikin rigima.
Ya ce “na gaya masa a wani lokaci daya gabata cewa, mutanen da ke biye da shi wakilai ne na wani dan siyasa a Legas. Na gaya masa ya fi dacewa ya horar da na tashi runduna a maimakon yin amfani da karnukan farauta, wadanda daga bisani ana iya karkatar da su da kudade.”
To sai dai duk da haka ya yi kira ga shugabanni a yankin na Yarbawa, daga sarakuna har ya zuwa gwamnoni, da su yafe wa Igboho kura-kuran da yayi, su kuma tsayu domin kare shi da rayuwarsa.
Yanzu haka dai Sunday Igboho yana wasan ‘yar buya da jami’an tsaron Najeriya da ke neman sa ruwa a jallo, bayan da ya arce a lokacin wani samame da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka kai a gidansa a makon nan da ya shige.
A cewar jami’an tsaron, Sunday Igboho ya sami arcewa ne a yayin musayar wuta da yaransa a gidan, to amma ta sami kashe biyu daga cikin yaran, ta kuma kama wasu 13, tare kuma da kwace makamai da albarusai da aka samu a gidan na sa.