Hukumar ta bayyana hakan ne a yayin taron hasashen yanayi karkashin tsarin sashen Sudan da Sahel da ya kunshi kasashe 17 a Abuja baboon birnin tarayyar Najeriya.
Ana sa ran daminar shekarar 2022 a kasashen yankin Sahel da Sudan ciki har da Najeriya ta kan-kama a watan Mayun mai zuwa a mizanin tsaka-tsaki kamar yadda alkaluman dandalin hasashen yanayi kasashen 17 karkashin shirin PRESAS na lokacin daminar wannan shekarar ya yi nuni.
Shugaban hukumar NIMET Farfesa Mansur Bako Matazu wanda Mailadi Yusuf ya wakilta ya ce makasudin taron kasashe goma sha bakwai shine bayyana yanayin da daminar bana zata kasance.
Mai bincike a kan yanayi a bangaren aikin noma na NIMET James Adamu Jampi, ya yi karin bayani kan yiyuwar samun Fari a wannan shekarar.
Dangane kuma da tanadi ake a birnin tarayyar Abuja don tunkarar daminar ta bana musamman ta fuskar daukan matakan shawo kan matsaloli masu alaka da ambaliyar ruwa, babban daraktar hukumar bada agajin gaggawa ta birnin Abuja wato FEMA, Abass Idris ya ce an tashi tsaye don duba kan ayyukan kamar yadda suka kamata kafin damuna ta kama.
A shekarar 2021 an sami ambaliyar ruwa a jihohin Kebbi, Legas, babban birnin tarayya da ma wasu jihohin kasar, lamarin da ya janyo kiraye-kiraye daga manoma da sauran masu ruwa da tsaki da su rika daukan matakan da suka dace akan lokacin.
Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5