Nijar Ta Kawo Karshen Kawancen Tsaronta Da Kungiyar EU

Janar Abdouramane Tchiani

Jiya litinin shugabannin sojojin Nijar suka bayyana cewa, za su kawo karshen ayyukan tsaro na Tarayyar Turai a kasar, bayan da a safiyar yau suka amince da karfafa hadin gwiwar soji da kasar Rasha.

Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Nijar ta ce za ta kawo karshen yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Nijar da kungiyar Tarayyar Turai dangane da aikin inganta karfin farar hula da ke Yamai mai suna EUCAP Sahel Niger.

Tawagar wacce aka kaddamar a shekarar 2012, tana tallafawa jami'an tsaron cikin gida na Nijar da hukumomi da masu zaman kansu.

Har ila yau, ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta sanar a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, "Jamhuriyar Nijar ta janye daga amincewar tura tawagar hadin gwiwar sojin Tarayyar Turai" a Nijar.

An kaddamar da kawancen sojan da aka fi sani da EUMPM a watan Fabrairu ne "bisa bukatar hukumomin Nijar", a cewar shafin yanar gizo na Tarayyar Turai.

An tsara shi ne don "ƙarfafa ƙarfin sojojin Nijar don shawo kan barazanar ta'addanci," in ji shafin yanar gizon.

A halin yanzu, shugabannin sojoji ne ke mulkin kasar tun bayan hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a watan Yuli, lamarin da ya janyo suka daga kasashen duniya.

Gwamnatin mulkin sojan dai ta nesanta kanta daga kawancen kasashen Turai na kut da kut a Jamhuriyar Nijar, musamman kasar Faransa, kuma ta kara kusanta kanta da makwabtanta Mali da Burkina Faso, wadanda bayan juyin mulkin baya-bayan nan da suma sojojin ke jagora sun kulla kawance da Rasha.

A halin da ake ciki kuma, tawagar kasar Rasha karkashin jagorancin mataimakin ministan tsaron kasar ta gana da hukumomin Nijar a birnin Yamai a ranar Litinin, inda kasashen biyu suka amince da karfafa hadin gwiwar soji.

Wata sanarwa da Burkina da Nijar suka fitar ta ce, "sun yanke shawarar ficewa daga G5 Sahel, gami da rundunar hadin gwiwa" daga ranar 29 ga watan Nuwamba.

A yanzu haka Chadi da Mauritania ne kawai suka rage a cikin kungiyar G5, da Tarayyar Turai ta fi daukar nauyin kudin tallafawa sojojinsu.

~ AFP