Tun shekaru takwas da suka wuce gwamnatin farar hula ta kulla yarjejeniya da kungiyar Tarayyar Turai ta yadda kasar ta Nijar dake yammancin Africa ke amsar makuddan kudade a hannun kungiyar wajen kange bakin haure dake ratsawa kasar zuwa Turai
To sai dai soke dokar da hukumomi a Nijar su ka yi ya sanya kungiyar Tarayyar Turai bayyana matukar damuwar ta akan wannan matakin na gwamnatin Nijar inda kwamishiniyar cikin gida ta Tarayyar Turai Ilva Johannasson tace akwai fargabar wannan matakin na Nijar ya baiwa tarin 'yan Africa dake son ficewa cikin kasashen su damar kwarara zuwa Turai.
Hukumomi a Agadas sun bayyana irin illar da dokar ta yiwa jihar ta fuskar tattalin arziki inda Jihar Agadas tayi asarar bilyoyin CFA a cewar Efad Hammado, mataimakin shugaban majalisar jihar Agadas.
Soke dokar hana safarar bakin haure da Nijar tayi kai tsaye, hakan yana nufin masu bulaguro zuwa turai ta hanya mai cike da hatsari zasu dawo ci gaba da hadadar su wanda wasu daga cikin al’ummar suka soma nuna shawa’ar zuwa Turai.
Wannan yarjejeniya tsakanin turai da Nijar ta taimaka wajen kange tarin kungiyoyin dake safarar bakin haure zuwa Turai ta hanyar ratsa sahara mai cike da hatsari da kuma teku. to sai dai a cewar 'yan kungiyoyin fararen hula irin su Kaocen Maiga soke dokar zai kawo ma Nijar kwanciyar hankali da kuma bunkasar tattalin arzikin ta.
jam’ar ta Tarayyar Turai tace, akwai bukatar kasashen turai su cimma matsaya ta bai daya a tsakanin su dangane da yadda zasu tunkari wannan matsalar.
Saurari rahoton :
Dandalin Mu Tattauna