Titin ofishin hukumar kula kaurar da jama’a ta IOM dake birnin Yamai ya cika da dauruwan ‘yan cirani ke bayyana takaicinsu dangane da abin da suka kira fatali da halin kuncin rayuwar da suka tsinci kansu ciki.
Yan ci ranin wadanda galibinsu mata ne da kananan yara na zaune ne bisa rashin sanin ranar da za a mayar da su kasashensu na asali, kamar yadda wata matashiya ‘yar kasar Saliyo ke bayyanawa Sashen Hausa cikin yanayi kuka har da hawaye.
Watanni a kalla shida kenan wadanan ‘yan cirani ke jibge a Nijer, ba tare da samun kulawar da ta kamata ba a cewar su, haka kuma ba wata sana’a abin da ke kara jefa su cikin damuwa saboda halin rashin tabbas a dangane da makomarsu.
Shaka Camara an tuso keyarsa daga kasar Libya, amma shi dan kasar Saliyo ne, ya ce a halin yanzu suna so a mayar da su kasashensu. Domin an yi musu alkawarin za a mayar da su gida amma babu wani yunkuri watanni shida kenan.
Shi ma wani dan Najeriya da aka dawo da shi daga Libya tare da iyalinsa a makon jiya, ya koka a game da yanayin da suke ciki a halin yanzu.
Yayin da ‘yan Jarida ke kokarin jin ta bakin hukumar IOM kan wannan lamari na halin da yan ciranin ke ciki, masu gadin ofishin sun hana kowa shiga hukumar, har ta kai ga cin zarafin wani dan Jarida kamar yadda wakilin Sashen Hausa Sule Muminu Barma ya ganewa idanunsa.
Jamhuriyar Nijer na matsayin wani sansanin da hukumar IOM ke girke dubban ‘yan ciranin da ake katsewa hanzari akan hanyarsu ta yunkurin zuwa Turai a kowace shekara, sai dai tsaikon da ake fuskanta kafin isar da su kasashensu na asali, kan haddasa tayar da jijiyoyin wuya wani zubin ma har da kazamar tarzoma.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Your browser doesn’t support HTML5