A cewar jaridar Punch da ta rawaito labarin, babban darakta kafafen labarai na zamani na Masari, El-Amin Isa, da kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, sun tabbatar da faruwar hatsarin, wanda ya auku a ranar Juma’a.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa wadanda lamarin ya rutsa da su tare da wasu mutane, suna kan hanyarsu ta zuwa mahaifar gwamnan, Kafur, domin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar da za a yi ranar Asabar.
Majiyoyin sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon rashin kyawon hanya a yankin.
Wata majiya ta ce, “Wadanda lamarin ya rutsa da su sun kusa isa wata gada da ke yankin ne a ranar Juma’a da daddare, sai suka afka a cikin wata mummunar hanyar, lamarin da ya tilasta wa motar da suke ciki kaucewa hanya ta fadi ta yita juyawa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsu.
Tuni wasu mutane uku da suka samu raunuka a hatsarin suke samun kulawa a babban asibitin Malumfashi, kafin daga bisani a kai su asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Katsina.
Tuni dai aka fara shirye-shiryen jana’izar su a ranar Asabar, kamar yadda kakakin ‘yan sandan ya ce an dauke gawarwakin fasinjojin da suka mutu daga wurin zuwa dakin ajiyar gawa a Katsina.
-Punch