Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arangama Tsakanin 'Yan Shi'a Da Ayarin Gwamnan Kaduna Ta Yi Sanadin Mutuwar 'Yan Shi'a 5 - Rahotanni


Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai)
Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai)

Shugabannin kungiyar Islamar nan da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ke mata jagoranci a Najeriya (IMN), wadda aka fi sani da Shi’a, sun yi zargin an kashe mambobinsu biyar tare da jikkata wasu da dama, a lokacin da suka yi arangama da ayarin motocin Gwamna Nasir El-Rufai a ranar Alhamis.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar IMN, Sheikh Aliyu Umar, wanda ya yi wa manema labarai karin haske a ranar Juma’a a Rigasa, karamar hukumar Igabi, ya ce kungiyar IMN za ta ja kunnen gwamnatin jihar kan kashe-kashen da ake yi wa mambobinta.

Amma rundunar ‘yan sandan Kaduna ta ce wasu fitinannu da ake zargin ‘yan kungiyar IMN ne suka harba makamai, da duwatsu kan ayarin motocin Gwamnan.

A cewar shugaban na Shi’ar, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a lokacin da ‘yan kungiyar IMN ke gudanar da zanga zangar lumana da suka saba yi domin neman a ba da fasfo din Sheikh Zakzaky na kasa da kasa domin samun damar tafiya.

Umar ya ce: “A ranar Alhamis, mun fito zanga-zangar da muka saba yi, saboda tuni aka saki jagoranmu (Sheikh Zakzaky), amma sun ki ba shi fasfo dinsa domin ya fita kasar waje don duba lafiyarsa. Don haka, mu kan fito mu tunatar da duniya cewa, har yanzu ana tauye wa shugabanmu hakkinsa.

To, a jiya, mun fito kamar yadda muka saba, kuma da muka fito daga titin Gwamna, daidai a Bakin Ruwa, muka gamu da ayarin Gwamnan, sai kawai jami’an tsaron da ke cikin ayarin suka bude mana wuta a gaban Gwamnan. Nan take, an kashe mutanen kirki kuma wasu sun sami munanan raunuka.

“Mun fara jin cewa, suna ikirarin mun tare hanya ne muka hana ayarin Gwamnan wucewa. Wannan ba gaskiya ba ne, ba mu tare hanya ba; kowa ya san haka, muna da tsari sosai kuma muna da mutanenmu da suke share hanya. Don haka, ba za mu iya tare ayarin motocin ba.

Jaridar The Nation ta labarto DSP Jalige na cewa: “Jami’an tsaro da ke tare da ayarin motocin Gwamnan Jihar Kaduna sun share hanyar Bakin Ruwa zuwa ta hanyar Rigasa da babbar hanyar Nnamdi Azikiwe bayan wasu ‘fitinannu da ake zargin ‘yan kungiyar Islama ta Nigeria (IMN) ne da suka kai wa ‘yan kasa hari kuma suka hana masu ababen hawa bin hanyar.

“Ko da fitinannun suka hango ayarin motocin sai suka fara harbe-harbe da jifar duwatsu suna harbin wasu motoci masu zaman kansu tare da wasu kalilan a cikin ayarin.

“Jami’an tsaro cikin kwarewa sun kama ‘yan tada zaune tsaye ba tare da amfani da karfi ba. An kama wasu daga cikin fitinannun da ake zargin 'yan kungiyar Islama ta Nigeria (IMN) ne kana ana ci gaba da bincike."

-The Nation

XS
SM
MD
LG